Ma’anar Sadarwa da Hanyoyinta na Gargajiya da na Zamani

Sadarwa

Maraba, yau za mu tattauna ne akan menene sadarwa, da kuma hanyoyin sadarwa na gargajiya har ma da na zamani.

Za kuma mu fara ne da na gargajiya.

Tun tale-tale Hausawa na da hanyoyin da suke bi na gargajiya wajen isar da sako walau daga wuri mara nisa ko mai nisa.

Duk da yanzu sakamakon zuwan Turawa da kuma samun cigaban kirkire-kirkiren fasaha an samu saukakan hanyoyin sadarwa wadanda suka fi sauki, amma dai al’ummar Hausawa suna da nasu hanyoyin.

Su kuwa hanyoyin da al’ummar Hausawa ke bi wajen isar da shi wannan sakon suna da ‘dan dama.

Hakika a wadancan lokutan babu yanar gizo, rediyo, talabijin, lasifika, wayar salula ko akwai tangaraho.

Amma sarakuna, da talakawansu akwai hanyoyin da suke bi a gargajiyance wurin isar da sako.

Menene Sadarwa

“Sadarwa dai na nufin isar da sako daga wani waje zuwa wani waje (wala’Allah wurin na da tazara ko bashi da ita).”

Hanyoyin Sadarwa na Gargajiya

A gargajiyance akwai hanyoyin da ake bi wajen isar da sako, wadannan hanyoyi sun hadar da;

1). Ganga

A zamanin da, ana yin amfani da ganga wurin isar da sako.

Ita dai ganga ana hadata ne da fatar dabbobi musamman ta akuya ko rago.

Kusan kowa dai ya sani, yayin da aka kada ganga tana da amsa kuwwa, to mutane da sunji tashin ganga a kwararo ko wata unguwa to sun san akwai labari.

Daga nan sai su dunguma yara da manya su rankaya wurin da suke jiyo amon gangar.

In ko a kwararo ne, sai su leko domin ganin me ke wakana.

2). Wasika

A kasar Hausa, wasika wani babban bigire ce ta isar da sako tsakanin talakawa, masu kudi har ma da masu sarauta.

Ana rubuta wasika da yaren Hausa (Ajami mai haruffan larabci) ko Fillanci, sai a tashi manzo ya haye doki ko ya taka a kasa ya kaita inda aka aikeshi.

Sai dai isar da sako a gargajiyance ta hanyar wasika na daukar lokaci (ya danganta da ratar da ke tsakanin wurare biyun).

3). Amsa Kuwwa

Da na ce amsa kuwwa, ba fa ina nufin lasifika ba.

Amsa Kuwwa dai wani karfe ne da ake kerashi da tama, yana da kwaroron baki kamar dai kwarkwaron silinda duk da bashi da rawun sosai.

Sai a samu wani karfen karami wanda bai kaishi girma ba, a rinka yawo da shi kwararo-kwararo ana dukansa da wannan karamin karfen yana amsar kuwwar.

Da zarar mutane sunji kuwwar nan sun san akwai wani sako da ake son isar musu a fadar mai gari ko wani wurin daban.

Haka kuma, kuwwar amsar kuwwa tana da amo mai karfi da daga nesa ma ana iya jiyota da zarar an buga.

4). Waka, Wake, Kasida, ko Roko

A zamanin da, a kasar Hausa, waka ko wake ko kuma kasida na daga cikin fitattun hanyoyin da ake bi wurin isar da sako walau tsakanin sarakai, attajirai, manoma, masoya da sauransu.

Mawaka ne da masu wake ke isar da sakon cikin salon balagar magana domin su zayyano surori da kyawawan dabi’un wanda suke son kambamawa ya musu alheri.

Haka ma masoya, su kan yin wake ga masoyansu domin su burgesu, su kuma fada musu abinda ke kunshe cikun ransu.

Misali: Masu sana’ar gambara, masu kada ‘dan kutuku da sauransu.

5). Guda

Guda hanya ce wacce mata ke amfani da ita wurin isar da sako musamman na farin ciki (walau a gidan biki, suna, ko kuma wani abin alkhairi ya faru).

Haka kuma, mata kan yin guda yayin da wani mai sarauta ya zo wucewa.

6). Yekuwa

Har zuwa yau, a yankunan karkara, ana yin amfani da hanyar yekuwa wurin isar da wani muhimmin sako (walau an yi sata, mai gari na kira ko akasin haka).

Wani mutum mai babbar murya shine zai zagaya unguwa-unguwa yana yin yekuwa tare da fadin sakon da yake son isarwa.

Kuma an fi yin yekuwa da daddare.

Dasa aya: Hakika juyin-juya-halin zamani ya kore da dama daga cikin wadannan hanyoyin sadarwa na gargajiya.

Amma duk da haka, har yanzu ana amfani da wasunsu a kauyuka.

Hanyoyin Sadarwa na Zamani

Tabbas akwai tarin hanyoyin da ake bi a zamanance wurin isar da sako cikin sauki ba tare da an sha wahala ba.

Har-ila-yau inda zama za na yi na yi maka bayani akan kowacce hanya daga cikinsu, to ba tantama da sai ka gaji da karantawa.

Bisa wannan dalili, shi yasa zan tsakuro sanannun cikinsu na yi muku bayaninsu a takaice.

1). Rediyo

Rediyo na daya daga cikin tsoffi kuma fitacciyar hanyar sadarwa da isar da dukkanin wani sako cikin sauri.

Sai dai yanzu haka, fasahar rediyo ta fara zama koma baya domin isar da sako, a yankin Afrika ne kadai har yanzu rediyo ke da matukar tasiri wurin isar da sako.

A kalla, an fi shekara 100 da samar da rediyo.

2). Talabijin

Talabijin har zuwa yanzu na cikin fitattun hanyoyin sadarwa na zamani a duniya, ta cikinta ake kallon finafinai, watsa labarai da rahotanni, yin hira da fitattun mutane da sauransu.

3). Wayar Salula

Wayar salula kowacce iri ce, na daga cikin hanyoyin sadarwa da isar da sako cikin sauri.

A zamanin da, an fi amfani da wayar salula wurin isar da sako tsakanin mutane kalilan.

Amma yanzu, sakamakon zuwar yanar gizo, ana iya isar da sako daga nan Afrika ya lulukar har sararin samaniya ta wayar salula.

4). Shafukan Sada Zumunta

Su ma shafukan sada zumunta na cikin jerin hanyoyin sadarwa na zamani, domin ana iya turawa da amsar sako ta cikin cikin sauri tsakanin mutum da ‘yan ‘uwa da abokan arziki, abokansa, da ma mutanen sassa daban-dabam na duniya.

5). Imel

Imel na daga cikin shahararrun hanyoyin sadarwa na zamani, wadanda ake aikawa da amsar sakon rubutu, bidiyo, audio, hotuna da sauransu.

Kammalawa

Tabbas hanyoyin sadarwa na gargajiya da na zamani suna da yawa. Wadanda su ka fi yawa ma su ne na zamani. Yayin da su na gargajiya za mu iya cewa yawansu ya danganta da irin al’ummar da suke amfani da su.

Namu na kasar Hausa dai ba su cika yawa ba, amma in ka kewaya wasu yankunan za ka samu wasu ma katon kararrawa Sarki ke sa wa a buga sai al’ummarsa su fahimci yana son ganinsu ne.

Ba kuma za mu sare muku gwuiwa ba akan kada ku cigaba da bincike, gaskiya ku cigaba da bincike domin binciko abin da mu ba mu iya ba.

Madallah.

Your trustworthy and reliable desk that uploads subtitles at Filmovity. For ad placement, broken download link or any issue, email us at [email protected]

MORE SUBTITLES